Welcome to Kada SMEs Hub
kada SMEs Hubkada SMEs Hubkada SMEs Hub
+234 803 640 3852
info@kadasmeshub.com
Mando, Kaduna
kada SMEs Hubkada SMEs Hubkada SMEs Hub

๐—”๐—บ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ ๐˜๐—ฎ๐—บ๐—ฏ๐—ฎ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ: ๐—ฆ๐—ต๐—ถ๐—ป ๐—บ๐—ฒ๐—ป๐—ฒ๐—ป๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐˜€๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ ๐—ธ๐—ฒ ๐˜๐˜€๐—ผ๐—ฟ๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ฏ๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฑ๐—ผ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐—ท๐—ถ?

  • Home
  • Builder
  • ๐—”๐—บ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ ๐˜๐—ฎ๐—บ๐—ฏ๐—ฎ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ: ๐—ฆ๐—ต๐—ถ๐—ป ๐—บ๐—ฒ๐—ป๐—ฒ๐—ป๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐˜€๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ ๐—ธ๐—ฒ ๐˜๐˜€๐—ผ๐—ฟ๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ฏ๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฑ๐—ผ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐—ท๐—ถ?

๐—”๐—บ๐˜€๐—ฎ๐—ฟ ๐˜๐—ฎ๐—บ๐—ฏ๐—ฎ๐˜†๐—ฎ๐—ฟ: ๐—ฆ๐—ต๐—ถ๐—ป ๐—บ๐—ฒ๐—ป๐—ฒ๐—ป๐—ฒ ๐—ฑ๐—ฎ๐—น๐—ถ๐—น๐—ถ๐—ป ๐—ฑ๐—ฎ ๐˜†๐—ฎ๐˜€๐—ฎ ๐—บ๐˜‚๐˜๐—ฎ๐—ป๐—ฒ ๐—ธ๐—ฒ ๐˜๐˜€๐—ผ๐—ฟ๐—ผ๐—ป ๐˜€๐—ฎ๐—ฏ๐˜‚๐˜„๐—ฎ๐—ฟ ๐—ฑ๐—ผ๐—ธ๐—ฎ๐—ฟ ๐—ต๐—ฎ๐—ฟ๐—ฎ๐—ท๐—ถ? Daga Tijjani Ahmad

Bayan nazarin raโ€™ayoyin mutane sama da 200 da suka bayar a wannan shafi, abu ya fito fili karara: ba dokar haraji ce ake tsoro kai tsaye ba, amma abin da mutane ke tsoro shi ne yadda ake tafiyar da ita da kuma wanda ke tafiyar da ita.

๐—”๐—ฏ๐˜‚๐—ฏ๐˜‚๐˜„๐—ฎ ๐—ด๐˜‚๐—ฑ๐—ฎ ๐˜€๐—ต๐—ถ๐—ฑ๐—ฎ ๐—ป๐—ฒ ๐˜€๐˜‚๐—ธ๐—ฎ ๐—ณ๐—ถ ๐—ณ๐—ถ๐˜๐—ผ๐˜„๐—ฎ:

1๏ธโƒฃ Rashin amincewa da gwamnati
Mutane da yawa sun yi imani cewa kudin haraji ba zai koma ga jamaโ€™a ba, sai dai a karkatar da shi. Ana yawan jin kalmomi irin su โ€œ๐’›๐’‚ ๐’‚ ๐’”๐’‚๐’„๐’† ๐’Œ๐’–๐’…๐’Š๐’โ€, โ€œ๐’Ž๐’๐’๐’Œ๐’†๐’š ๐’…๐’†๐’š ๐’˜๐’๐’“๐’Œ, ๐’ƒ๐’‚๐’ƒ๐’๐’๐’ ๐’…๐’†๐’š ๐’„๐’‰๐’๐’‘โ€.

2๏ธโƒฃ Rashin cikakken bayani da wayar da kai
Wasu da dama sun amsa cewa basu fahimci dokar ba. Abin da suka sani jita-jita ne, bidiyo ko tsoratarwa daga wasu da su kansu ma basu fahimci dokar sosai ba.

3๏ธโƒฃ Darasin cire tallafin man fetur (subsidy)
Mutane sun ce an sha alkawura a baya amma ba a ga sauyi a rayuwa ba. Wannan ya sa duk wani sabon tsari ana kallonsa da ido na shakku.

4๏ธโƒฃ Tsananin halin rayuwa
A lokacin da mutane ke fama da hauhawar farashi, rashin wuta, rashin tsaro da aikin yi, duk wani abu da ya shafi karin cire kudi yana kara tsoratar da su.

5๏ธโƒฃ Tsoron zalunci wajen aiwatarwa (enforcement)
Wasu na tsoron haraji ba saboda biyan harajin ba, sai saboda tsoron danniya, task-force, ko amfani da bank data ta hanyar da ba ta dace ba.

6๏ธโƒฃ Damuwar โ€˜yan kasuwa da masu kananan sanaโ€™oโ€™i
Akwai tsoron cewa za a ciri haraji akan turnover ba akan riba ba, sannan a dora nauyin bookkeeping da tsadar compliance da zai iya kashe kasuwanci.

๐Ÿ‘‰ Muhimmin sakon da wannan raโ€™ayi ya nuna shi ne:
Mutane ba sa kin haraji idan suna ganin adalci, gaskiya, bayani a fili, da amfanin da zai dawo gare su.

Idan ana son sabuwar dokar haraji ta yi nasara:
1. Dole a fara da bayani mai sauฦ™i ga jamaโ€™a,
2. A gina aminci da gaskiya,
3. A nuna inda kudin haraji ke tafiya,
4. A kuma kare talaka da โ€˜yan kasuwa daga zalunci.

Haraji ba shine matslarba, amma rashin amana da rashin bayani su ne manyan matsaloli.

โ€”
Dr. Tijjani Ahmad
(Chartered Accountant | Tax & Investment Analyst)

Leave A Comment