Welcome to Kada SMEs Hub
kada SMEs Hubkada SMEs Hubkada SMEs Hub
+234 803 640 3852
info@kadasmeshub.com
Mando, Kaduna
kada SMEs Hubkada SMEs Hubkada SMEs Hub

Sabowar Dokar Haraji ta Nijeria

Shin ka shirya tunkarar sabuwar dokar haraji da zata fara aiki nan da kasa da kwanaki arbain da biyar (45)? Dada Ado Mohammed Abubakar, FCA, FCTI

Duk da gwamnati bata wayar da kan mutane yadda ya kamata. Ko kuma ince ta fi mai da hankali akan wasu tsiraru . Mu sani cewa rashin sanin doka ba zai taba kare mutum a gurin hukuma ba.

Ya zama dole ga ‘yan kasuwar mu su fara engaging masana domin fahimtar wadannan dokokin don gujewa fadawa hannun bata garin ma’aikatan haraji a lokacin da dokokin su ka fara aiki.

Da yawa abubuwan da muke ji a teburin mai shayi a game da dokokin ba gaskiya bane. Fahimtar dokokin shine zai sa mu gane haka.

Mu sani cewa:

1. Babu haraji akan jari/ciniki ko kudin da yake ajiye a banki.
2. Haraji akan riba kawai (profit/income).
3. Mune da kanmu zamu lissafa kasuwancin mu sannan mu ware ribar da mu samu. Mu kuma lissafa harajin da ya kamata mu biya gwamnati akan wannan ribar. (self-assessment).
4. Gwamnati zata biyo baya ne kawai idan bayanan da ta tattara ya nuna cewa akwai shakku akan bayanan da muka bayar.
5. Sahihan bayanai da hujjojin da muka ajiye zasu zama kariya a gare mu lokacin bincike.
6. Akwai abubuwan da doka ta yarda ka cire daga cikin riba kafin biyan haraji.
7. Akwai hukunci/tara masu tsanani ga wanda bai bi wadannan sababbin dokokin ba.

Domin kare kanka/kasuwancin ka akwai bukatar ka inganta mu’amilar ka ta hanyar:

1. Ajiye sahihan bayanai akan shige da fice na kudaden ka.
2. Ajiye duk wata shaida da zata tabbatar da bayanan shige da fice na kudaden ka.
3. Turawa da bayanan ka zuwa hukumomin haraji akan lokacin da doka ta tanada.
4. Tuntubar masana domin samun shawarwari akan yanda zaka samu ragin harajin da zaka biya.

Mu sani wadannan dokoki suna da incentives da dama da zasu rage mana radadin haraji, amma wanda ya sani ko ya fahimta ne kawai zai amfana.

Allah ya sa mu dace.

Ado Mohammed Abubakar, FCA, FCTI

Leave A Comment