Kafin ka canza daga BN zuwa RC โ ga gaskiyar da ba a gaya maka ba!
Mutane da yawa suna gaya min an basu shawara su chanja rijistar kasuwancin su daga “Business Name (BN) zuwa “Registered Company” (RC).
Hujjar da kawai masu basu shawara suke amfani da ita shine mai rijistar “RC” ba zai biya haraji ba har sai jumillar cinikin sa a shekara (Annual Turnover) ya haura N100 Miliyan. Ba sa sanar da su sauran abubuwan da doka ta gindaya akan masu rijistar “RC” kamar haka:
1. Dole ne duk shekara ka tura da bayanan ka zuwa reshen hukumar haraji ta kasa da ta ke jihar da ofishin ka yake. Ko da kuwa baza ka biya haraji ba. Ana tura bayanan ne ta kafar yanar gizo ta hukumar haraji ta kasa.
2. Dole ne ka dinga ajiye sahihan bayanan kasuwancin ka. Kuma ya kasan ce kana ajiye bayanai na shekarun da suka wuce saboda Tax Audit.
3. Idan baka tura bayanan ka a lokacin da doka ta kayyade ba akwai tara ta N100,000 a watan farko, kuma za’a ci gaba da kara tarar N50,000 akan N100,000 ta farko duk wata har sai ka tura da bayanan (Returns).
4. Akwai tarar N50,000 idan baka ajiye sahihan bayanai ba.
5. Sannan idan cinikin ka ya haura N100 miliyan yawan harajin da zaka biya da rijistar “RC” ya kusa biyun wanda zaka biya da rijistar “BN”
6. Sannan bayan haraji na 30% akwai kuma 4% Development Levy da mai rijistar “RC” zai biya.
Kafin ka chanja rijistar ka daga “BN” zuwa “RC” ka tuntubi masana su duba yanayin kasuwancin ka domin baka shawara.
Ado Mohammed Abubakar, FCTI, FCA
